Akwai gidaje biyu, ɗaya a Dogon Dutsi, ɗaya a Yamai domin sabke baƙi.

Mambobin Tarbiyya Tatali da sauran abokan hulɗa da ke zowa daga Faransa, suna zaman wani lokaci domin zartar da wasu ayyukan ƙungiyar;kuma zaman otal bai dace ba saboda tsadarshi, balle ma in zaman lokaci mai tsawo ne. Amma kuma sai sun daure sosai san nan su iya ƙare zamansu a irin halin da ƴan ƙasar suke ciki. Don haka muka shirya gidajen namu na Dogon Dutsi da Yamai, daidai yadda suke iya rayuwa a cikin su ba tare da sun damu sosai ba. Kowane gida yana da ɗaki huɗu (4) masu iya karɓar mutum har takwas (8).

Tarbon masu neman ƙarin horo

Matasa ƴan ƙasar Faransa masu neman ƙarin horo suna zowa da dama su yi ƴan watanni a Nijar don ƙarfafa ayyukan ƙungiyar dangance da irin karatun da suke yi ko wani aiki na kansu. Idan suka zo, muna karɓar su a gidajenmu inda muka tanada duk abun da ya dace masu.

Gidan ƙungiyar a Dogon Dutsi

Har shekara ta 2003, Tarbiyya Tatali ba ta da gida a Dogon Dutshi, cibiyar yankin Arewa,kuma jaha ce inda mafi yawan ayyukanmu suke. To, gidan sabke abokai ya bada ɗaki domin shawarwarinmu, kuma ana gina ɗakin littattafai bisa tarihi da al’adun Nijar.

Maison de l’amitié à Dogondoutchi
Dogon Dutsi