Nijar ƙasar afirka ce da take nesa da ruwan teku wajen kudu ga hamadar sahara.
Maƙwabtanta su ne Aljeriya da Libiya a Arewa, Najeriya da Bini a kudu, Mali da Burkina Faso a yamma, Cadi a Gabas
Tutar Nijar
Ƙabilun al’ummar ƙasar Nijar
- Hausawa su ne mafi yawa cikin al’ummar ƙasar Nijar. Ana samun su cikin yankuna daga tsohon kogi na yankin Arewa zuwa yankin Damagaram. Rabon ƙasashe na mulkin mallaka shi ya raba hausawan ƙasar Nijar da na ƙasar Najeriya.
- Zabarmawa da suke zaune Yammacin ƙasar Nijar su ne na biyu wajen yawa.
- Fullani su ne ƙabila ta uku. Tun lokacin da, makiyaya ne. Ana samun su ko’ina cikin ƙasar Nijar. Asalinsu udawa ne. Amma sannu-sannu suna komawa mazauna wuri guda.
- Barebare ana samun su daga yankin Damagaram (Zandar) har zuwa ƙasar Cadi.
- Abzinawa da Buzaye suna zaune a yankin Arewa cikin ƙasar Nijar.
- Tubawa suna rayuwarsu wajen iyaka da ƙasar Cadi.
- Larabawa ana samun su yankunan Tawa da Zandar.
- Gurmawa suna zaune iyaka da Nijar da ƙasar Burkina Faso.
- Buduma suna rayuwa cikin tsibiran kogin Cadi.
Carte du Niger
